NYSC ta musanta jita jitar da ake yadawa cewa za a tura matasan na NYSC zuwa Nijar domin dawo da dimokuradiyya a kasar

Hukumar kula da matasa masu yiwa kasa Hidima NYSC ta musanta jita jitar da ake yadawa cewa za,a tura matasan na NYSC zuwa Kasar Nijar dan dawo da mulkin Demokaradiya a Nijar din.

Mai magana da yawun hukumar ta kasa Mr Eddy Megwa, a wata takarda da ya fitar aka rabawa manema labarai domin mayar da martani akan wani Bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta dake nuna cewa za,a tura matasa masu yiwa kasa Hidima Nijar dan suyi sulhu da sojojin kasa a dawo da mulkin Demokaradiya,yana mai cewa labarin kirkirarre ne.

Ya nemi matasa masu yiwa kasa Hidima dasu kwantar da hankalinsu yana mai cewa babu wata hukuma ko kungiya da zata tura matasan zuwa Nijar. Hukumar ta NYSC ta kuma yi barazanar daukar matakin shari,a akan wandanda suka yada labarin na karya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *