Kungiyar Likitoci ta bayyana tsunduma zanga-zangar da kuma mamaye asibitocin gwamnatin tarayya

Kungiyar Likitoci masu Neman kwarewa (NARD) ta bayyana tsunduma zanga-zangar da kuma mamaye asibitocin gwamnatin tarayya da ke fadin kasar nan.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a yammacin jiya Asabar , wadda a halin yanzu kungiyar ta na kan gudanar da yajin aikin gama-gari, ta ce zanga-zangar kowace rana za ta fara ne daga ranar Laraba 9 ga watan Agustan 2023 da misalin karfe 10:00 na safiya.

Sanarwar na zuwa ne bayan zaman da ajalisar kolin kungiyar ta cimma a ranar Asabar sannan aka lika zuwa adireshin babban Sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na tarayya.

Sanarwar na dauke sa hannun shugabanta da sakataren kungiyar, Dakta Orji Emeka Innocent da Dakta Chikezie Kelechi.

NARD ta ce matakin an dauka ne domin tabbatar da matsa kaimi wajen ganin an biya musu bukatunsu da ke jibge a hannun ma’aikatar kiwon lafiya da gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *