Tinubu ya kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta a Abuja

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta a yankin Gwagwalada na birnin tarayyar Abuja.

Aikin da kamfanin Mai NNPCL tare da hadin gwiwar wasu kamfanonin makamashi na kasashen waje ne suka kulla don biyan bukatar samar da karin iskar gas da zai taimaka wajen bunkasa harkar samar da wutar lantarki a kasar nan.

A lokacin kaddamar da gagarumin aikin na wutar lantarkin, Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna farin cikinsa, yayin da yake yi wa ‘yan Najeriya jawabi a bikin kaddamar da daya daga cikin muhimman aikin samar da ababen more rayuwa acewarsa.

Ana sa ran wannan aiki zai samar da Megawatt 350, wanda ya kasance kashi na farko na aikin gaba daya wanda ake matukar bukata.

Shugaban Kasa Bolq Ahmad Tinubu ya ce makamashi shi ne mafi muhimmancin abin da ‘dan adam ya gano a cikin shekaru dubu daya da suka gabata, a don haka ya ce Dan Adam ba zai iya rayuwa mai inganci ba, ba tare da wutar lantarki ba saboda haka ya ce Najeriya na buƙatar makamashi ainun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *