Sheikh Rijiyar Lemu ya buƙaci shugaba Tinubu ya guje wa ɗaukar matakin soji kan gwamnatin sojin Nijar

Malamin addinin nan sheikh Muhd Sani Umar Rijiyar Lemu ya buƙaci shugaba Tinubu ya guje wa ɗaukar matakin soji kan gwamnatin sojin Nijar.

Malamin ya ce ya kamata Najeriya ta yi tunani a kan dangantakar da ke.tsakaninta da ƙasar da kuma al’ummar jamhuriyar Nijar.

Da yake tsokaci kan juyin mulkin a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Jumu’a, Malamin ya ce dangantar da ke tsakanin Najeriya da Nijar ta zarce maƙotaka.

Sheikh Rijiyar Lemo ya ce ɗaukar matakin soji da yaƙi zai ƙara dagula lissafi ne, ya ƙara jefa al’umma cikin wahalhalu baya ga wahalhalun da suke fama da su.

Tuni dai ECOWAS ta umarci sojojin su maida wa hamɓararren shugaban ƙasa, Muhammed Bazoum mulki cikin mako ɗaya ko kuma ƙungiyar ta ɗauki matakin soji a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *