Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama mutane fiye da 60 a cikin mako 2

Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta kama mutane fiye da 60 a cikin mako biyu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a yayin gabatar da wadan da ake zargin.

Ya ce wadanda aka kama sun hada da ‘yan daba da masu safarar kwayoyi sai kuma masu kwacen babura da motoci.

Kiyawa ya ce an samu muggan makamai da kwayoyi da kuma kayayyakin da aka sace wa jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *