Majalisar dokokin Zamfara ta tabbatar da naɗin mutane 18 da Gwamna Dauda Lawal ya aika mata a matsayin kwamishinoni

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutane 18 da Gwamna Dauda Lawal ya aika mata a matsayin kwamishinoni.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Malam Nasiru Biyabiki ya fitar a Gusau.

Tun da farko, shugaban masu rinjaye na majalisar, Malam Bello Mazawaje ya gabatar da kudirin a kan bukatar gwamnan na tantancewa tare da tabbatar da sunayen wadanda ya naɗa, daga bisani kuma Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Malam Aliyu Ango ya goyi bayan kudurin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *