Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a matsayin wadda za’a naɗa kan muƙamin minista.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a matsayin wadda za’a naɗa kan muƙamin minista, inda ya maye ta da sunayen mutum biyu.

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aikawa majalisar kuma ya karanta yayin wani zama a wannan rana ta Juma’a.

Sunayen mutum biyu da Shugaba Bola Tinubu ya aikawa majalisar da suka haɗarda Festus Keyamo da kuma Dr. Mariya Mahmud Bunkure.

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika da jerin sunayen mutum  biyu na mutanen da yake so Majalisar Dokokin ƙasar ta tantance domin naɗawa a matsayin ministoci.

A cikin jerin sunayen akwai tsofaffin gwamnonin jihohi, da ƴan majalisa da kuma matasa.

Daga cikin matasan da jerin sunayen ya ƙunsa, wanda yafi ɗaukar hankali shine na Maryam Ibrahim Shettima daga jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *