NLC tayi barazanar sake komawa zanga-zanga a ranar 14 ga watan Agusta

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) tayi barazanar sake komawa zanga-zanga a ranar 14 ga watan Agusta matukar Gwamnatin Tarayya bata janye karar data shigar da ita ba.

Kungiyar tayi gargadin ne bayan taron Majalisar Zartarwarta daya gudana a Abuja a ranar Alhamis.

A ranar Laraba ne dai Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Shari’a ta Kasa ta maka ’yan kwadagon bisa zargin raina kotu saboda tace a baya an hana su shiga zanga-zanga

A cewar sanarwar wacce shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, ya fitar, NLC tace Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da Kotun Ma’aikata sun cigaba da yarda ana amfani dasu a matsayin “makiya Dimokuradiyya.”

NLC tace duk da bayan tattaunawarta da Shugaban Kasa, Bola Tinubu, a ranar Laraba, inda suka yarda su dakatar da zanga-zangar, zasu sake dawowa da ita matukar gwamnatin bata janye karar ba.

Joe Ajaero ya kuma ce, “daga cikin abubuwan da suka amince dasu akwai bukatar dakatar da zanga-zangar da suka fara ranar Laraba Gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dai sun fara zanga-zanga ne a fadin Najeriya don nuna bacin ransu kan cire tallafin mai da sauran manufofin tattalin arzikin da suka kira “masu gallazawa talakawa” da Shugaba Tinubu ya aiwatar tun bayan darewa karagar mulkin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *