Ba’a nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa tace ba tayi zaben tumun dare ba’a nada tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar APC ne bayan da aka share makonni ana yada jita-jitar nada shi mukamin.

A wani taron majalisar koli na jamiyyar APC a karkashin jagorancin shugaba Tinubu,  ta ayyana Ganduje a matsayin wanda ya maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa Ibrahim Kabir Masari, yace gogewar tsohon gwamnan na kano kan dabarun siyasa ne suka duba wajen dora shi kan kujerar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *