Atiku ya gargadi shugabannin ECOWAS kan hada baki da sojoji domin dawo da dimokaradiyya a Nijar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gargadi shugabannin kungiyar ECOWAS, kan hada baki da sojoji domin dawo da dimokaradiyya a Jamhuriyar Nijar.

Atiku, a wata sanarwa daya sanyawa hannu da kansa  a Abuja, ya dage cewa rikicin Nijar na bukatar dorewar huldar diflomasiyya.

A cewarsa, tsoma bakin sojoji a Nijar zai haifar da tashin hankali a yankin yammacin Afirka, lamarin daya jawo hankalin duniya ga makwabciyarta Najeriya.

Rikicin siyasa a Nijar ya fara ne a ranar 28 ga watan Yuli, bayan da shugaban dakarun tsaron kasar Janar Abdourahamane Tchiani ya hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum tare da ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

Kungiyar ECOWAS a karkashin sabon shugabancin Bola Tinubu na Najeriya, tayi alkawarin zage damtse kan masu yunkurin juyin mulki tare da kakabawa jamhuriyar Nijar takunkumi mai tsanani.

Sai dai kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea a halin yanzu sunbi sahun gwamnatin mulkin sojan Nijar, suna masu gargadin daukar matakin soji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *