‘Yan kwadagon Najeriya sun dakatar da zanga-zanga bayan ganawa da Tinubu

Sa’o’i 24 kacal bayan fara zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur a fadin kasar nan wanda aka fara a ranar Laraba.

Kungiyar kwadagon ta dakatar da shirinta na yajin aiki a fadin Najeriya.

Mun ta tattaro cewa Shugaban Kungiyar Kwadago Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Arise News a safiyar ranaf Alhamis din nan.

Ya ce shugabannin yan kwadago da tun farko suka gana da shugaban kasa Bola Tinubu sun fitar da wasu alkawurra kan wasu batutuwan da aka tattauna yayin taron domin aiwatar da su cikin gaggawa.

Ya bayyana dakatar da yajin aikin ya samo asali ne a kan haka.

Mun ruwaito a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Talata, kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kamar yadda aka tsara tun farko, bayan wata ganawa da ta yi da gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *