Uwargidan shugaban kasa ta kaiwa Buhari ziyarar ban girma a gidansa

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu,ta kaiwa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa na Daura da ke jihar Katsina.

Uwargidan shugaban kasar wadda ta samu rakiyar uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ta ce, sun kai ziyarar ne domin duba tsohon shugaban kasar, dubi da yadda ya dauke so tamkar ‘ya’yanshi.

Uwargidan shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Busola Kukoyi, ya fitar, tayi addu’ar Allah ya karawa Buhari lafiya, ya kuma kara masa nisan kwana don goyon baya ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma cigaba da taimakawa Nijeriya baki daya.

Anasa jawabin yayin ziyarar, tsohon shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa, inda yace ziyarar da takai domin ganin yadda yake rayuwa bayan sauka daga mulki, ta bata mamaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *