Shugaban INEC ya kalubalanci yan jarida da su dinga bayyana hakikkanin labarin da suka samu a yayin zabe

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, farfesa Mahmood Yakubu ya kalubalanci yan jarida da su dinga bayyana hakikkanin labarin da suka samu a yayin zabe domin yin haka zai taimaka wajen inganta tsarin gudanar da zabubbuka a kasar nan

Farfesa Yakubu Mahmoud wanda yayi wannan kiran a jihar Legas, a yayin wani taro da hukumar ta shirya don yin nazarin yadda zabubbukan shekara ta 2023 suka gudana a jihar Legas ya kara da cewa hukumar sa ba tada da shakka akan yadda zabubbukan shekara ta 2023 suka gudana a dukkanin fadin kasar nan.

Shugaban na hukumar zabe, ya kuma bayyana cewar a kullum yumun kofar hukumar sa a bude ta ke ga sauraron dukkanin wanda ke da wata shawara da za ta taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zabe a Najeriya.

A karshe Farfesa Yakubu mahmoud ya yaba da irin tarin goyin bayan da hukumar sa ta samu daga kafafan yada labarai musamma ma wajen wayar da kan yan najeriya akan al’amurran zabe da kuma abinda ake bukatar su sani dangane da zabe a mataki dabam dabam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *