Majalisa ta ɗage zaman da take yi na tantance mutanen da Tinubu ya aika musu don naɗa su a matsayin ministoci.

Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗage zaman da take yi na tantance mutanen da Shugaba Tinubu ya aike musu don naɗa su a matsayin ministoci.

Zuwa yanzu Majalisar ta tantance rukunin farko na mutum 28 da Fadar Shugaban Ƙasa ta aika musu tun a makon da ya gabata.

Majalisar ta karɓi cikon mutum 19 a yammacin yau, sannan ta ɗaga zaman zuwa Juma’a don ci gaba da tantance su.

Mutum biyar aka tantance a yau, mutum tara ranar Talata, da kuma 14 a ranar farko.

Ƙarin sunayen ya sa jimillar adadin ministocin ta zama 47

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *