Gwamnatin Kano ta amince da fitar da naira biliyan 7 domin gudanar da wasu ayyuka a fadin jihar

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da naira biliyan bakwai domin gudanar da wasu manyan ayyuka a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Halilu Dantiye ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwa na mako guda biyu da aka gudanara  ranar Alhamis.

Dantiye yace an amince da kudaden da ayyukan ne a zaman taro na biyu dana uku na majalisar domin magance bukatun jama’a na samar da ababen more rayuwa cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa an amince da sama da Naira biliyan 1.6 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje don kammala ginin sabon ofishin hukumar bincike da bayanai a gidan gwamnati

Sauran ayyukan sun hada da gina hanyar ruwa a bakin kogin Jakara-Kwarin Gogau, da sayan na’urori da akayi amfani dasu   da kuma kananan gadaje na Hukumar Raya Birane ta jihar Kano (KNUPDA) da na’urorin kwasar shara na hukumar kula da tsaftar muhalli 11 a manyan birane.

Hakazalika, an amince da Naira miliyan 779 ga Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta biyan kudin wutar lantarki na tsawon watanni uku, da sayan metric ton 600 na Aluminum Sulfate don amfani dasu a wuraren kula da magunguna, samar da sinadarai, da kula da ayyukan fasaha na yau da kullum na masana’antar.

Dantiye ya bayyana cewa Ma’aikatar Sufuri ta samu amincewar kashe sama da Naira miliyan 37 domin gyara motocin da KAROTA ta ajiye, da farfado da ayyukanta da kuma gyara Cibiyar Tuki ta Jihar da ke kan hanyar Zariya.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa an baiwa ma’aikatar muhalli izinin gudanar da aikin share magudanun ruwa a duk shekara kan kudi naira miliyan 5, yayinda hukumar kula da tsaftar muhalli (REMASAB) ta karbi sama da naira miliyan 658 a matsayin kudaden gudanar da aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *