NLC ta kammala ganawa da Tinubu a fadarsa.

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun kammala ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

An yi ganawar ‘yan sa’o’i bayan mambobin ƙungiyar sun yi zanga-zangar ƙasa baki ɗaya don yin tir da cire tallafin man fetur.

Yayin zanga-zangar, ‘yan ƙwadagon sun shiga zauren Majalisar Dattawan Najeriya, inda Mai Tsawatarwa na Majalisa Sanata Ali Ndume ya tarɓe su.

Zuwa yanzu ba a bayyana abin da ɓangarorin suka tattauna ba, da kuma ko sun cimma wata matsaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *