Wani hatsarin jirgin saman shelikwafta mai saukar ungulu ya afku a unguwar Oba Akran da ke Ikeja a jihar Legas.
Mun tattaro cewa Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a kusa da wani reshe na bankin United Bank for Africa da ke can.
PUNCH ruwaito cewa Kawo yanzu dai ba a iya tantance asarar rayukan da hatsarin ya janyo ba da kuma bayanan da aka samu masu rauni har zuwa lokacin da hada wannan rahoton.
Ana kuma dakon masu bayar da agajin gaggawa a wurin da lamarin ya faru.