NLC: “Baza mu fasa yin zanga-zanga ranar laraba”

Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC, sun ce zanga-zangar da suka shirya yi a ranar Laraba kan yaki da hauhawar farashin man fetur da sauran manufofin Gwamnatin Tarayya na nan daram.

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a daren Talata a Abuja.

Ya ce rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa na cewa kungiyar za ta dakatar da gudanar da shiga zanga-zangar ba gaskiya ba ne.

Tun da fari Aminiya ta rawaito Sakataren NLC na kasa na cewar NLC na iya dage zanga-zangar da ta shirya shiga a ranar Laraba.

Kungiyoyin dai sun shirya zanga-zangar ce don nuna rashin goyon bayansu ga abin da suka kira da “tsauraran manufofi tattalin arziki” na Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren kungiyar na kasa, Emma Ugbaja, ne ya bayyana hakan ga manema labaran Fadar Shugaban Kasa, bayan an dage tattaunawar da suka tsara yi da gwamnatin Tarayya a dakin taro na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *