Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministoci 14 cikin 28 da ya aika mata.

Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministoci 14 cikin 28 da Shugaban kasar Bola Tinubu ya aika mata, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike.

 To sai dai ‘yan siyasa da masana harkokin shar’ia  sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan cancantar ministocin.

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike wanda yana daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar adawa wadanda Tinubu ya zabo domin ba su kujerar Minista ya sha alwashin zai baiwa marada kunya idan ya fara aiki a matsayin Minista a Gwamnatin Tinubu.

To sai dai Sanata Sahabi Ya’u, daga Jihar Zamfara, ya ce majalisar ta tantance Ministoci 14 a maimakon 16 da Majalisar ta yi niyan tantancewa.

Sahabi ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya zabi wadanda ya ke ganin sun cancanta wajen yi wa kasa aiki musamman ma ta bangaren hada kan kasa.

Sahabi ya ce talakan da ke Najeriya ya dauki Tinubu a matsayin wani wanda zai share masu hawaye wajen fidda Najeriya halin da ta ke ciki.

Ya ce Shugaba Tinubu yayi kokarin nuna cewa shi mai bin doka ne wajen kawo sunayen ministoci a cikin watani biyu na mulkin sa kamar yadda doka ta tanada kuma wannan abin yabawa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *