A ranar Alhamis mai zuwa ake sa ran tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban riko na jam’iyar APC

A ranar Alhamis mai zuwa ake sa ran tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban riko na jam,iyar APC ta kasa.

Sannan za,a tabbatar da tsohon mai magana da yawun majalisar dattawa ta 9 Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam,iyar na Riko.

Hakan zai tabbatu ne bayan kammala taron majailsar zartaswa na kasa na jam,iyar APC.

A ranar Lahadi data gabata ne aka maye gurbin manyan Allunan da suke dauke da hotunan tsohon shugaban APC na kasa Adamu Abadullahi dana Toshon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a harabar shelkawatar APC ta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *