“Sama da ‘yan matan Najeriya 2,000 da ake fataucin su ne suke kasar Mali a halin yanzu”. – NAPTIP

Hukumar hana fataucin bil adama ta kasa NAPTIP ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewa sama da ‘yan matan Najeriya 2,000 da ake fataucin su ne suke kasar Mali a halin yanzu.

Kwamandan shiyyar Benin na hukumar ta NAPTIP, Nduka Nwanwene, wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa hukumar ta samu bayanan sirri cewa ana safarar ‘yan mata daga kasar Mali zuwa jihar Edo domin yin karuwanci.

Nduka ya yi magana ne a yayin bikin ranar yaki da fataucin mutane ta duniya na shekarar 2023 a Benin, tare da taken “Ku kai ga duk wanda aka yi fatauci, kada ku bar kowa a baya.”

Ya ce hukumar ta NAPTIP, karkashin Farfesa Fatima Waziri-Azi, tana samun ci gaba a fannin hukunta manyan masu fataucin mutane, da ci gaba da gyare-gyare ta hanyar karfafa wa wadanda suka tsira da rayukansu guiwa da koya musu sana’o’i.

Nduka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da hukumar NAPTIP wajen bayar da tallafi domin magance matsalar fataucin bil adama tare da bayar da gudunmuwa wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *