“Mun fara aikin bibiyar wadanda suka yi mu’amala da masu dauke da cutar Diptheria” – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta fara aikin bibiyar wadanda suka yi mu’amala da masu dauke da cutar nan ta Diptheria, yayin da cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 31 cikin 44 na jihar.

Likitan da ke kula da cutuka masu yaduwa a jihar, Dakta Abdullahi Kauran-mata, wanda ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai, ya ce sama da majinyata 100 ne ke kwance a asibiti, yayin da kimanin majinyata 2,000 da aka basu kulawa kuma suka warke aka sallame su.

Farfadowar cutar diphtheria, a cewarsa, ana iya danganta shi da cutar COVID-19, wadda ta haifar da kalubale da kuma rushewar rigakafin yau da kullun da ake yi ga yara kanana.

Kauran-mata ya ce, a kwanan baya, hukumar NCDC ta fitar da jerin sunayen da kuma sabbin bayanai da ke bayyana adadin jihohin da abin ya shafa, tare da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da mace-macen kananan yara.

Rahoton ya bayyana jihar Kano a cikin jihohin da ke da yawan masu fama da cutar ta diphtheria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *