A yau ne Majalisar dattawan Najeriya zata fara zaman tantance mutane 28 da Tinubu ya mika mata, domin amincewa ya nada su ministoci.

A yau Litinin ne majalisar dattawan Najeriya take fara zaman tantance mutane 28 da Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya mika mata, domin amincewa ya nada su ministoci.

Haka kuma ana sa ran shugaban kasa zai aika da wasu karin sunayen kasancewar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya.

Daga sunayen da Shugaban kasar ya mika wasu jihohin suna da mutum biyu yayin da wasu ba su da ko daya.

Bisa al’ada dai majalisar kan amince da wasu mutanen salun alun, da gaisuwa kawai yayin da wasu kuma kan sha tambaya.

Sanata Mohammed Ali Ndume, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya shaida cewa Majaisar za ta yi taza da tsifa don tabbatar da ta sauke nauyin da ke kanta yadda ya kamata.

Sai dai ya ce kamar yadda aka saba bisa al’ada, wannan karon ma ba za a bata lokaci wajen tantance duk wanda ya taba zama Sanata a cikin sunayen da aka aika musu ba, domin idan har ka taba zama Sanata, to kuwa ka cika duk wani sharadi na zama minista ma. Ya ce kafin a kawo sunayen ma dama jami’an tsaro na gudanar da bincike a kansu, domin tabbatar da cewa babu wata matsala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *