Orji Uzor Kalu ya bayyana rokonsa ga NLC kan shirin yajin aiki da take yi nan kusa.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Abia ta Arewa sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana rokonsa ga kungiyar kwadago kan shirin yajin aiki da take yi nan kusa.

Sanata Kalu ya bayyana cewa, akwai bukatar kungiyar ta NLC ta yi duba da irin wahalar da ‘yan kasar ke ciki tare da daga kafa da shirin yajin aikin.

Hakazalika, ya yi tsokaci da cewa, shi kansa mai kamfani ne da ke da mutanen da ke aiki a karkashinsa, don haka ya san zafin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

A cewar Kalu, yajin aikin da NLC din ke shirin yi zai iya durkusar da tattalin arzikin Najeriya, wanda a yanzu ma tuni ya riga ya shiga halin ni ‘ya su.

Da yake karin haske game da halin da mutane ke ciki a kasar nan, dan majalisar ya bayyana cewa, babu mai kudi ko talaka, kowa na shan wahala a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *