Kungiyar Likitoci ta jaddada matsayinta na ci gaba da gudanar da yaji aiki

Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya  ta jaddada matsayinta na ci gaba da gudanar da yaji aiki har sai gwamnatin ƙasar ta biya mata buƙatunta.

Hakan na zuwa ne a yayin da ƙungiyar ke shiga kana na huɗu tun bayan fara yajin aikin sai-baba-ta-gani a ƙasar.

Shugaban kungiyar Dakta Emeka Oji ya bayyana hakan a lokacin ani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yajin aikin har sai an samu ani gagarumin ci gaba daga ɓangaren gamnatin tarayya, domin duba buƙatun ƙungiyar.

Dakta Oji ya kuma ce kamtin gudanarar kungiyar tasu na yin kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su gaggauta biya wa kungiyar bukatunta domin kauce wa ci gaba da yajin aikin, lamarin da ya ce ka iya kawo cikas ga fannin lafiyar ƙasar.

Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) na da mambobi 15,000 daga cikin likitoci fiye da 40,000 da ake da su a ƙasar.

To sai kungiyar ce ƙasai ke cikin yajin aikin, yayin da babbar kungiyar likitocin ƙasar ta (NMA) ba ta cikin yajin aikin.

To sai Dakta Oji ya ce za su ci gaba da tuntuɓar ƙungiyar likitocin ƙasar ta NMA domin ganin ta bi sahunsu wajen shiga yajin aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *