Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na kawar da cutar polio a jihar sakamakon rahotanni dake tabbatar da sake bullar cutar a wasu daga Cikin jihohin kasar Nan ciki har da Nan jihar kano.
Gwamnatin ta bayyana aniyarta na yaki da cutar tare da bada dukkanin gudummawar data kamata ga ma’aikatar Lafiya ta jihar kano domin ganin an tabbatar da kawar da burbushin cutar a fadin jihar Kano Baki Daya . Gwamnan Kano Eng Abba Kabir Yusuf Wanda ya samu wakilcin matemakinsa Kuma Kwamishinan kanana Nan hukumomi na jihar Kano comrade Aminu Abdussalam gwarzo yayin kaddamar da Digon allurar polio da ya gudana a sabar din Nan a karamar hukumar gabasawa ya bayyana cewa
anasa jawabin Kwamishinan lafiya na jihar kano Dr Abubakar labaran Yusuf ya Yi Kira ga hukumomin lafiya dasuyi amfani da tagomashin da akaibawa Yara domin Kara Kare garkuwar jikinsu yadda ya kamata tare da shawartar Iyaye dasu tabbatar sun bada hadin Kai ga ma’aikatan lafiya yayi wannan rangadi na allurar ta polio.
Wakiliyarmu ta ofishin matemakin gwamna Sadiya Tsoho Salisu Kosawa ta bayyana Mana cewa aron ya samu halartar wakilan hukumomin lafiya na Duniya Kwamishinani daban daban hakimin gabasawa da dagatai da masu unguwanni.