Ana sa ran yau lahadi Ecowas zatayi taron gaggawa a Abuja domin tattauna batun juyin mulkin sojoji a Nijar.

A yau Lahadi ne ake sa ran ƙungiyar Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas zatayi wani taron gaggawa  a birnin tarayya Abuja domin tattauna batun juyin mulkin sojoji  a jamhuriyar Nijar.

Shugaban kasa  Bola Ahmed Tinubu wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar ta Ecowas shine zai jagoranci taron, wanda ake sa ran shugabannin ƙasashen yammacin Afrika za su halarta.

Tuni dai shugaban na Ecowas cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya yi Allah wadai da juyin mulkin, tare da alƙawarta cewa ƙungiyar Ecowas tare da sauran ƙasashen duniya za su yi duk abin da ya dace wajen ganin sun kare dimokradiyya.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar za kuma ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin mulkin farar hula ya ci gaba da wanzuwa a yankin yammacin Afirka.

Cikin sanarwar taron na Ecowas da ta fito daga fadar shugaban na Najeriya, ta ce mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres a tattaunawar da suka yi daban-daban da shugaba Tinubu, sun bayyana goyon bayan Amurka da kuma MDD kan matsayin ƙungiyar Ecowas da shugaban na Najeriya.

Za dai ayi taron ne alhalin sojojin da sukai juyin mulkin na ci gaba da tsare shugaba Muhammad Bazoum da suka kifar da gwamnatinsa.

Tuni dai ƙasar Faransa da ƙungiyar EU suka sanar da dakatar da ayyukan tallafi da suke bai wa Nijar sakamakon juyin mulkin da sojojin suka yi.

Ita ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU a nata ɓangare, ta ce ta bai wa sojojin wa’adin kwanaki 15 su koma barikokinsu, su kuma maido da mulkin farar hula a ƙasar da ke yankin yammacin Afirka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *