Shettima: “Shugaba Tinubu zai farfado da Najeriya daga jinyar da take ciki”.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya musamman mazauna kasar Rasha cewa kasar a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta sake yin aiki

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai ya fitar a ofishinsa, Mista Olusola Abiola, ta ce mataimakin shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne da yammacin ranar Juma’a a birnin St Petersburg a wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Rasha

Shettima, wanda ke magana a kan matsalolin da al’ummar yankin suka shiga, ya ce ku tabbata nan da watanni 9 zuwa 12 masu zuwa za a samu sauyi cikin gaggawa a tattalin arzikin Nijeriya

Da yake magana kan kokarin da gwamnati ke yi na sake farfado da tattalin arzikin kasar, VP ya ce mun zo nan ne

Don halartar taron kasashen Afirka da Rasha kuma muna kokari don ganin an kammala ginin katafaren kamfanin karafa na Ajaokuta tare da farfado da kamfanin Aluminum Smelter na Najeriya. (ALSCON)

Ku tabbata cewa idan akwai abu guda daya da Shugaba Tinubu zai yi wa ‘yan Najeriya wasiyya to Ajaokuta ce kamar yada thenation ta ruwaito

Zan dawo Rasha, za mu gudanar da wannan tsari, kuma shugabana, maigidana Bola Ahmed Tinubu ya sadaukar da kai ga Ajaokuta da ALSCON

Mun fara tattaunawa, kuma za mu ga cewa wadannan kamfanoni biyu sun tashi, ba mu da wani zabi da ya wuce mu dawo dasu kan aiki

Da yake karin haske game da yadda Najeriya za ta kawo sauyi, VP, ya ce gwamnatin Tinubu za ta yi amfani da dimbin albarkatun  da Allah ya hore mata don dora kasar nan kan turbar ci gaba mai dorewa

Don haka Manufarmu ita ce horar da ’yan Najeriya 1,000,000 kan fasahar zamani domin su dogara da kansu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *