“Mun fara tantance takardun ministoci 28 da Tinubu zai naɗa”. – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ta fara tantance takardun ministoci 28 da shugaba
Bola Ahmed Tinubu zai naɗa.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Abdullahi
Gumel ne ya faɗi haka yayin hira da yan jarida a Abuja ranar Jumu’a.

Ya ce ana umartan dukkan ministocin su ziyarci ofishin hadimin Tinubu kan harkokin
majalisa domin tantance takardun karatunsu daga ranar Jumu’a 28 zuwa Lahadi, 30 ga
watan Yuli.

Sanata Gumel ya yi bayanin cewa a wannan wa’adin na kwana 2 za a tantance tare da
kacewr takardun ministoci gabanin majalisa ta fara tantance su ranar Litinin 31 ga watan
Yuli.

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, shugaban kasa Tinubu ya aike
sunayen mutane 28 da zai naɗa a matsayin ministoci ga majalisar dattawa.


Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen bayan ya karɓa daga
shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *