El-Rufai: “Ban yi wa na kasa da ni adalci ba idan na maimaita kujerar minista”

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa babu adalci ya maimaita kujerar minista a yayin da shekarunsa suka ja.

El-Rufai ya yi wannan furuci ne a wani tsohon bidiyo da aka nada yana tattaunawa da wasu mutane da ba a iya tantance su ba.

Ana iya tuna cewa, El-Rufai ya rike mukamin Ministan Abuja daga shekarar 2003 zuwa 2007 a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo.

Sai dai a halin yanzu, sunan tsohon gwamnan ya sake bayyana a cikin jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya mika wa Majalisar Tarayya domin tantancewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *