Tinubu, ya mayar da martani kan rikicin siyasa a Nijar

Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kuma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da martani kan rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar

Tinubu ya jaddada cewa ECOWAS ta lashi takobin tabbatar da mulkin dimokuradiyya da tsarin mulki a kasar ya shimfida tare da gargadin sojojin da ke kwadayin mulki ko ta halin kaka su shiga taitayinsu.

Tinubu ya jaddada cewa yankin zai tsaya tsayin daka wajen goyon bayan zababbiyar gwamnati a Nijar.

Ya jaddada muhimmancin kiyaye dimokuradiyya ga al’ummar Nijar da zaman lafiya da cigaban yankin yammacin Afirka baki daya.

Yace Shugabannin ECOWAS ba zasu amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga halattacciyar gwamnatin Nijar ko wani yanki na yammacin Afirka ba.

Nijar kasa ce daba tada ruwa a yammacin Afirka, wadda ta fuskanci juyin mulki hudu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960, da kuma yunkurin juyin mulki da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *