Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da suyi hakuri da fahimtar juna, musammanma matasa, inda ya bada tabbacin cewa wahalhalun da ake ciki a halin yanzu zasu bada damar samun ci gaba, daidaito da kuma hada-hadar tattalin arziki.
Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a fadar gwamnatin tarayya yayinda yake karbar bakuncin shugabannin matasan jam’iyyar APC na kasa daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja
Ta cikin wata sanarwa da mai bawa shugabar kasa shawara na musamman Dale Alake ya fitar.
Shugaban ya shaidawa matasan cewa gwamnatinsa zata sanya su a cikin harkokin mulki, inda ya kara da cewa “babu wani hukunci da zai yi wuya gwamnatinsa ta dauka don cigaba da hadin kan al’umma.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa za tayi duk abinda ya dace don fadada harkokinta domin a samu karin mata da matasa.
A cewarsa, za’a yi hakan ne, ta hanyar ‘hulɗa da cibiyoyin bada lamuni don bada ƙananan rancen kuɗi a cikin rangwame’ don ayyukan tattalin arziki tsakanin ‘yan ƙasa. Tunda farko anasa jawabin, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Hon. Abdullahi Dayo Isra’ila, ya shaidawa shugaban kasar cewa, a matsayinsu na wakilan dukkanin bangarorin matasa na jam’iyyar, sun zone taya shi murnar nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben daya gudana tare da neman a saka su cikin rusassun hukumomi da ma’aikatun gwamnati