“Nan bada jimawa ba zamu sake tura karin sunayen minisoti 13 ga Majalisar Dattawan kasar”. – Gbajabiamila

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Femi Gbajabiamila yace nan bada jimawa ba, zasu  sake tura karin sunayen minisoti 13 ga Majalisar Dattawan kasar.

A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutune 28 da zai nada a matsayin ministoci.

‘Yan Najeriya sun jima suna dakon fitar da jerin sunayen ministocin yayinda  wa’adin da doka ta tanada na mika sunayen yake gab da karewa.

A cewar Gbajabiamila, akwai yiwuwar shugba Tinubu ya kirkiri wasu sabbin ma’aikatu

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, yace  da yiyuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kirkiro wasu sabbin ma’aikatu da zasu zama kari kan wadanda ake da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *