FG ta amince da biyan N25,000 ga likitoci da sauran ma’aikantan lafiya na tarayya

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan alawus na makudan kudade har N25,000 ga likitoci da sauran ma’aikantan lafiya na Tarayya.

Wannan amincewar na zuwa ne bayan likitocin sun shiga yajin aiki saboda rashin daidaito a tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya

Shugaban hukumar kula da albashi na Tarayya, Ekpo Nta ne ya tabbatar da amincewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu akan biyan kudaden a Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta kuma yi cikakken bayani akan wasu daga cikin matsalolin likitocin da ya jawo yajin aikin

Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan korafin da suka ta yiwa Gwamnatin Tarayya ba tare da biya musu bukatunsu ba.

Kungiyoyi da dama na barazanar shiga yajin aikin saboda wasu matsalolin su na daban da suke nema a wurin gwamnatin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) tayi barazanar shiga yajin aiki a watan Agusta kan karin albashin ma’aikata tun bayan cire tallafin mai a kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *