Yajin aikin da kungiyar likitoci ya saka harkokin kiwon lafiya a fadin kasar cikin halin ha’ula’i.

Yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fara a ranar Laraba ya saka harkokin kiwon lafiya a cibiyoyin jama’a a fadin kasar cikin halin ha’ula’i.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar likitocin Dr Orji Emeka Innocent ya shaida wa BBC cewa mambobinsa sun gama da duk wani zabin da suke da shi na magance rikicin.

A asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da ke jihar Kano, an ce mutane su komar ‘yan uwansu marasa lafiya gida saboda babu likita da zai duba su.

A babban birnin tarayya Abuja, karamar ƙungiyar ta ce suna jiran sanarwa daga ƙungiyar ta kasa kafin su shiga yajin aikin, don haka suna kula da marasa lafiya.

A Legas kuma, likitoci na ci gaba da kula da majinyatan da aka kwantar da su amma ba sa karban sabbin marasa lafiya.

Likitoci masu neman ƙwarewa wadanda ke da kaso mafi tsoka na likitoci a manyan asibitocin Najeriya, sun ce suna yajin aiki har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu na albashi da walwala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *