Tinubu ya fitar da jerin sunayen ministocinsa

Ana ci gaba da tsokaci a kan ƙunshin sunayen mutum 28 da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattijan ƙasar don neman amincewarta kafin naɗa su ministoci.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godwill Akpabio ne ya gabatar da sunayen a gaban zauren majalisar.

Matakin na zuwa ne kwana ɗaya kafin ƙarewar wa’adin wata biyu da tsarin mulkin Najeriya ya gindayawa shugaban ƙasa ya tabbatar da naɗa ministocinsa.

Miƙa sunayen ga alama zai rage ka-ce-na-ce da jita-jitar da aka yi ta yaɗawa ne kawai game da sabbin ministocin da Tinubu zai yi aiki da su. Amma har yanzu da sauran tsalle, don kuwa daga lissafi kawai za a iya fahimtar cewa sunayen ba su cika ba.

Akwai jihohin da har yanzu ba a gabatar da sunan wakili/wakilansu a sabuwar majalisar ministocin Tinubu da zai kafa ba.

Bisa tanadin tsarin mulki, kowacce cikin jihohin Najeriya 36 da Abuja, babban birnin ƙasar, suna da damar samun aƙalla minista ɗaya,

Bugu da ƙari, an ga jihohin da suka samu minista biyu a jerin sunayen da aka gabatar kamar Hannatu Musawa da Arch Ahmed Ɗangiwa daga Katsina da Farfesa Ali Pate da Yusuf Maitama Tuggar daga Bauchi, sai Betta Edu da John Eno daga jihar Kuros Riba.

Jerin sunayen kamar yadda aka yi tsammani ya ƙunshi mutanen da suka fito ba kawai daga jam’iyya mai mulki ba, an ga har da sunayen ‘yan adawa musamman daga babbar jam’iyyar hamayya ta PDP kamar Nyesom Wike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *