Daga Satumbar 2023 gwamnati za ta fara ba wa dalibai rance.

Gwamnatin Tarayya ta ce daga watan Satumbar wannan shekara za ta fara ba wa dalibai rance.

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Ayyuka na Musamman, Dele Alake, ya kara da cewa gwamnati za ta bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa dalibai masu karamin karfi.

Alaka ya ce dokar bai wa dalibai rance da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu za ta fara aiki gabanin shiga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba.

Sai dai kuma bai ce uffan ba game da matakai ko shirye-shiryen da gwamnatin ta yi domin tabbatar da hakan.

Ya kuma nesanta Gwamnatin Tarayya da karin kudin rajista da sauransu da jami’o’inta suka yi, inda ya ce, har kwanan gobe ba a biyan kudin makaranta a jami’o’in, don haka babu gaskiya a rahoton da wasu kafofin yada labarai suka wallafa cewa gwamnatin ta kara kudin makaranta a jami’o’inta.

Ya bayyana cewa, “Shugaba Tinubu zai ci gaba dayin tsayuwar daka domin cika alkawarinsa na ganin kowane dan Najeriya komai matsayinsa ko karfin iyayensa, ya samu ilimin gaba da sakandare.”

Dele Alaka ya sanar da hakan ne a ranar Laraba, bayan wata kafar yada labarai ta ruwaito cewa Jami’ar Legas, mallakin Gwamnatin Tarayya ta kara kudin karatu da ninki 10 daga N19,000 zuwa N190,250 ga daliban fannin likitanci, dangoginsu kuma zuwa N140,250.

Amma ya ce duk da cewa ba a biyan kudin makaranta, makarantun “sukan karbi kudin rajista da na dakunan kwana, na dakunan gwaje-gwaje da sauransu, kuma ya danganta da kowace jami’a; amma wannan ba kudin makaranta ba ne.”

Hadimin shugaban kasan ya ce wannan ne wasu suka dauka a matsayin kudin makaranta, amma ba haka abin yake ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *