Ana cigaba da fargaba kan yunkurin juyin mulki A Nijar

Rahotanni dake fitowa daga jamhuriyar Nijar dake makwaftaka da kasar Najeriya, na nuni da cewa jami’an tsaron fadar shugaban kasar sun rufe gidaje da ofisoshin shugaba Mohamed Bazoum.

Matakin na zuwa ne biyo bayan yunkurin juyin mulkin da ake zargin sojojin kasar na yi.

A halin da ake ciki dai jami’an na kusa da shugaban kasar da iyalansa sun ce komai na cikin tsari kuma ana tattaunawa da manyan sojojin kasar.

Kasar Afirka ta Yamma ta fuskanci juyin mulkin soji hudu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960 da kuma wasu yunƙuri na neman mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *