Kotu ta bayar da belin Emefiele

Babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Legas ta bayar da belin gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da aka dakatar kan kudi naira miliyan 20, bayan ya shafe makonni shida a hannun hukumar ‘yan sandan sirri ta DSS.

Mista Emefiele ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa a kai guda biyu na mallakar bindiga guda daya da kuma harsashi 23, zargin da rundunar ‘yan sandan sirri ta gabatar.

A ranar Talata ne gwamnan bankin da aka dakatar ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya biyo bayan umarnin kotu na gurfanar da shi ko kuma a sake shi daga hannun hukumar DSS.

A watan da ya gabata ne dai hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sanar cewa Emefiele na hannunta kwana guda bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa daga aiki.

A hukuncin da aka yanke a ranar Talata, alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Mista Emefiele a gidan yari na Ikoyi, da ke Legas har sai an kammala cika ka’idojin belinsa.

An dage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *