“Gwamnatin tarayya za ta sassauta radadin tashin farashin man fetur a Najeriya” – George Akume

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya ce gwamnatin tarayya za ta sassauta radadin tashin farashin man fetur a Najeriya sakamakon cire tallafin da ta yi.

A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a karshen mako, Akume ya sake fitar da wasu matakai da gwamnatin Bola Tinubu ke dauka na cika alkawarin da jam’iyyar APC, ta daukarwa al’ummar kasa.

A jawabinsa na rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur wanda nan take ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki a fadin kasar nan.

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, wanda shi ma ya kara farashin man fetur a gidajen sayar da man, ya ce an samu canjin ne saboda yanayin kasuwa.

Da yake magana game da lamarin, Akume ya ce Tinubu ya shafe shekaru aru-aru yana nazarin hanyoyin da zai bi domin maido da kasar nan kan turba, kuma shugaban yana kan magance wannan matsalar.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da gwamnati za ta bayyana wani shiri na inganta tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *