An nada Abdu maikaba a matsayin sabon kochin kungiyar kwallon kafa ta Kano pillers.

Gwamnatin jihar Kano ta nada Abdu maikaba sabon kochin kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars.

Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da nadin yau a gidan gwamnatin jaha.

Gwamna Abba Kabir Wanda ya Sami wakilcin mataimakinsa komared Aminu Abdussalam gwarzo yace lokaci yayi da gwnanatin jahar kano zatayiwa kungiyar garbawul  Hadi da gyara filin wasan kungiyar inda zata koma Kan kadaminta na shekarun baya hakan yasa gwamnatin ta nada kabiru me kaba a matsayin sabon kochin kungiyar domin mayar da ita Kan matsayin ta .

A jawabinsa Shugaban riko na kungiyar ta Kano pillers babangida Ibrahim little ya Yabada tabbacin kungiyar zata bada mamaki.

Wakiliyar mu ta ofishin Mataimakin gwamna Sadiya Tsoho Salisu Kosawa ta rawaito Mana cewa sabon kochin kungiyar Abdu me kaba yayi alkawarin duk me yiyuwa wajen sauke nauyin da aka daura Masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *