Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Najeriya domin wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wasu taruka da za ayi a kasashen Italiya da Rasha.
Sanata Kashim Shettima zai halarci taron da za ayi a birnin Rome a Italiya da wani a sinti Petersburg a kasar Rasha kamar yadda aka sanar a jawabi a jiya.
Darektan yada labarai na ofishin Mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, ya nuna Shettima ya bar Najeriya tun Lahadi, zai sauka a babban birnin Rome.
Mista Abiola yana mai cewa mataimakin shugaban kasar zai kasance tare da sauran shugabannin Duniya a taron STM da za ayi a Rome.
Shettima ya tabbatar a shafinsa na Facebook cewa sun isa Italiya.
An dai shirya zaman ne kan harkar abinci, za a dauki kwanaki biyu daga Litinin zuwa Laraba ana taron.
Sanarwar ta kara da cewa Sanata Shettima zai jagoranci wani zama da za ayi mai taken “Dabarun samar da kudi wajen kawo sauyi a harkar abinci a Najeriya.”
Abiola ya ce kungiyar abinci ta Duniya watau FAO da ke karkashin majalisar dinkin Duniya, da irinsu IFAD da WFD ne su ka shirya wannan taro.
Ana gama wannan taro kuma Shettima zai wuce birnin St. Petersburg a Rasha domin ya wakilci shugaban kasa wajen taron hadin-kan Rasha da nahiyar Afrika.
Shi kuma wannan taro zai dauki tsawon kwanaki hudu, sai ranar Asabar za a kammala.
Mataimakin shugaban Najeriyan zai hadu da sauran shugabannin kasashen Rasha da na nahiyar Afrika wajen ganin yadda za a bullowa matsalolin kasar nan.
Yayin zaman za a tattauna a kan harkar kasuwanci tsakanin jami’an gwamnatocin Najeriya da Rasha, bayan nan tawagar za ta dawo garin Abuja.