Adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo a Kaduna ya kai 17.

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo a jihar Kaduna ya kai mutum 17.

An kuma gano mutane 68 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗn jihar zuwa ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin jihar ta Kaduna ta tabbatar.

Daga cikin adadin, an samu rahoton mutuwar mutane 14 a Kafanchan da karamar hukumar Jema’a, yayin da uku kuma suka mutu a karamar hukumar Makarfi.

Babban jami’in kula da cututtuka na ma’aikatar lafiya ta jihar, Dokta Jeremiah Daikwo, yaceana dakon sakamakon samfuri guda 20 da ma’aikatar ta tattara kuma ta aika domin a yi gwaji.

Mutane 48 da aka kwantar da su kuma na samu kulawar da ta dace.

Daikwo ya bayyana cewa majinyata 12 suna kwance a babban asibitin Makarfi, 35 kuma a babban asibitin Kafanchan, sai kuma majiyyaci ɗaya a cibiyar lafiya a matakin farko ta Kubau.

Dangane da matakin da ma’aikatar ta ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar, babban jami’in kula da cututtukan ya ce ma’aikatar ta kara kaimi wajen neman waɗanda suka kamu da cutar da kuma kai su zuwa cibiyar kiwon lafiya domin ba su kulawa. Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta kara zage damtse wajen sa ido a kananan hukumomin jihar 23, ta hanyar aiki tare da magidanta da kuma shugabannin al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *