Za a gurfanar da Emefiele a ranar 5 ga watan Yuli.

Babbar Kotun tarayya mai zama a birnin ikko ta sanya ranar 25 ga watan Yuli,a matsayin ranar da za’a gurfanar da dakataccen gwamnan babban banki kasa na (CBN), Godwin Emefiele.

A cewar rahotanni za’a gurfanar da Emefiele a gaban Kotun ne domin fuskantar shari’a kan tuhumar mallakar haramtattun makamai.

Alkalin Kotun mai shari’a Nicholas Oweibo ne ya sanya ranar fara sauraron ƙarar bayan jinkirin hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) wajen gabatar da tuhume-tuhume kan wanda ake zargi.

A ranar 13 ga watan Yuli, hukumar DSS ta shigar da tuhume-tuhume biyu kan Emefiele a Kotun wanda suka ƙunshi mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta kuma zargi dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya da mallakar alburusai guda 123 waɗanda ba suda lasisin haƙƙin mallaka kamar yadda doka ta tanada.

Emefiele ya shiga hannun DSS ne tun bayan lokacin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar dashi daga matsayin gwamnan CBN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *