Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashe a Filato

Rundunar Sojin Kasarnan ta kaddamar da wata runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashe a  jihar Filato, wanda aka yiwa lakabi da Hakorin Damisa ta 4.

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ne ya kaddamar da sabuwar rundunar  a karamar hukukumar Mangu ta jihar domin kawo karshen hare-hare da kisan jama’a ba gaira babu dalili a Mangu da wasu sashi na jihar baki daya.

Rikicin baya-bayan nan a yankin yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 300 a karamar hukumar Mangu da kewaye cikin watanni biyu sakamakon hare-hare mabanbanta da ‘yan bindiga suka kai.

Bayan kaddamar da sabuwar rundunar ta Hakorin Damisa, shugaban sojin kasa na Najeriyar ya kuma yi wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a wata makarantar firamare dake garin na Mangu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *