Jonathan ya bukaci shugabannin kasashen duniya dasu rungumi zaman lafiya ta hanyar bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya

Tsohon shugaban kasa  Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci shugabannin kasashen duniya dasu rungumi zaman lafiya ta hanyar bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya da kuma shugabancin son jama’a a kasashensu

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne  a kasar Cambodia, a wajen taron shugabanni  kasa da kasa, wanda kungiyar ‘yan majalisar dokokin kasa da kasa don zaman lafiya da Cibiyar hangen nesa ta Asiya suka shirya.

Da yake jawabi kan bukatar tabbatar da dimokuradiyya ta gaskiya, Dr. Jonathan ya bayyana cewar,idan aka baiwa ‘yan kasa damar gudanar da zabensu cikin ‘yanci, zasu kada kuri’a don samar da dawwamammen zaman lafiya da cigaba mai dorewa da kuma tsayawa tsayin daka wajen yaki da danniya, kama-karya da cin zarafin ‘yan kasa.

Tsohon shugaban kasar wanda yayi magana kwana guda gabanin gudanar da babban zaben kasar Cambodia

A wata sanarwa da Ikechukwu Eze, mai taimakawa tsohon shugaban kasar kan harkokin yada labarai ya fitar yace, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci  kasashen duniya  dasu samar da hadin kai da dogaro da kai domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *