Da yiwuwar majalisar dattawa ta ɗage shirinta na tafiya hutun shekara

Da yiwuwar majalisar dattawa ta ɗage shirinta na tafiya hutun shekara yayinda ake tsammanin isowar sunayen ministocin shugaban ƙasa domin tantance wa.

Rahotanni na cewar  Sanatocin na tsammanin shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aiko da sunayen ministocin a farkon mako mai zuwa.

Ɗaya daga cikin shugabannin majalisar dattawa yace ana tsammanin Sanatoci zasu tafi hutunsu na shekara daga ranar 27 ga watan Yuli, zuwa watan Satumba.

Sai dai a cewarsa, mambobin majalisar dattawan a shirye suke su riƙa zama kowace rana domin tabbatar da sun tantance Ministocin da aka naɗa, koda hakan zai jawo ɗaga tafiya hutun da mako ɗaya.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, yace majalisar nada isasshen lokacin duba buƙatar shugaban kasa kafin tafiya hutu.

A cewarsa, har yanzu ba’a sanar da ranar tafiya hutun shekara ba’a majalisar dattawa

Adaramodu ya jaddada cewa majalisar tarayya zata yi abinda ya dace kuma ba zata yi kuskuren baiwa yan Najeriya kunya ba.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu ya tura sunayen ministocin ga hukumar yan sandan farin kaya (DSS) da hukumar yaƙi da cin hanci da  rashawa (EFCC) domin tantance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *