Tinubu, ya taya al’ummar Musulmin ƙasar nan murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmin ƙasar nan murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Cikin wani sako da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya buƙaci Musulmi da su koyi da ɗabi’un Manzon Allah Annabi Muhammad SAW da suka haɗa da hakuri da juriya da kuma karfin imani.

Ya ce duk rintsi, shi da muƙarrabansa sai sun cika alkawuran da suka ɗauka wa ƴan Najeiya, duk da irin tarin wahalhalu ake ciki a yanzu.

Daga karshe ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yin addu’a da kuma rokon Allah wajen samun saukin matsaloli da ƙasar ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *