Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta yi Allah wadai da munanan ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar nan inda ta yi gargadin cewa duk wanda hukumar ta kama za a gurfanar da shi a gaban kuliya, kuma zai fuskanci hukuncin dauri.
Da take sanar da hakan a Legas, yayin wani taron wayar da kan jama’a kan illolin shan miyagun kwayoyi Darakta Janar ta hukumar NAFDC, Farfesa Christianah Adeyeye ta ce a halin yanzu jami’an tsaro na hukumar na gudanar da aiki tare a duk fadin kasar nan.
Ta kuma bayyana cewa babu wani mai laifi da zai tsira daga fuskantar cikakken fushin Doka.