Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya halarci babban taron gidauniyar ci gaban jihar Katsina na 2023 da aka gudanar a gidan gwamnati Katsina a safiyar Laraba.
Wannan shi ne karom farko da Buhari ya bayyana a bainar jama’a bayan mika ragamar mulki ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.
Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ne, ya tarbi tsohon shugaban a wajen taron tare da manyan jami’an gwamnati.